Wap & Web Maker Tutorial
SEARCH
SURATUL BAQARAH (surah no 2) - Hausa Qur an

SURATUL BAQARAH (surah no-2)

June 22, 2020adminsuratul baqarah1

Surah ta 2

Ayah 1-29
1; A. L. M.
2; Wancan ne Littafi, babu shakka a cikinsa, shiriya ne ga masu takawa.
3; Wadanda suke yin imani game da gaibi, kuma suna tsayar da salla, kuma daga abin da Muka azurta su suna ciyarwa.
4; Kuma wadanda suke yin imani da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar daga gabaninka, kuma game da Lahira suna yin yakini.
5; Wadannan suna kan shiriya, daga Ubangjinsu, kuma wadannan su ne masu cin nasara.
6; Lalle ne wadanda suka kafirta daidai ne a kansu, shin ka yi musu gargadi ko ba ka yi musu gargadi ba, ba za su yi imani ba.
7; Allah Ya sa hatimi a kan zukatansu, da a kan jinsu, kuma a Kan ganin su akwai wata yana; kuma suna da wata azaba mai girma.
8; Kuma akwai daga mutane wanda yake cewa: "Mun yi imani da Allah kuma da Yinin Lahira." Alhali kuwa su ba muminai ba ne.
9; Suna yaudarayya da Allah da wadanda suka yi imani, alhali ba su yaudarar kowa face kansu, kuma ba su sakankanchewa!
10; A cikin zukatansu akwai wata cuta. Sai Allah Ya karamusu wata cuta, kuma suna da azaba mai radadi saboda abin da suka kasance suna yi na karya.
11; Kuma idan aka ce musu: "Kada ku yi barna a cikin kasa," sukan ce: "Mu masu kyautatawa kawai ne!"
12; To, lalle ne su, sune masu barna, kuma amma ba su sansancewa.
13; Kuma idan aka ce musu: "ku yi imani kamar yadda mutane suka yi imani," sukan ce: "Za mu yi imani ne kamar yadda wawaye suka yi imani?" To, lalle ne su, su ne wawaye, kuma amma ba su sani.
14; Kuma idan sun hadu da wadanda suka yi imani,sukan ce: "Mun yi imani. "Kuma idan sun wofinta zuwa ga shaidanunsu, sukan ce: "Lalle ne muna tare da ku: Mu masu izgili, kawai ne."
15; Allah Yana yin izgili gare su kuma Yana taimakon su a cikin batarsu, suna dimuwa.
16; Wadannan su ne wadanda suka sayi bata da shiriya, sai fataucinsu bai yi riba ba, kuma ba su kasance masu shiryuwa ba.
17; Misalinsu shi ne kamar misalin wanda ya hura wuta, to, a lokacin da ta haskake abin da yake ghfensa (na abin tsoro), Allah Ya tafi da haskensu, kuma Ya bar su a cikin duffai, ba su gani.
18; Kurame, bhbaye, makafi, saboda haka ba su komowa.
19; Ko kuwa kamar girgije mai zuba daga sama, a cikinsa akwai duffai da tsawa da walkiya: suna sanyawar yatsunsu a cikin kunnuwansu daga tsawarwakin, domin tsoron mutuwa. Kuma Allah Mai khwayewa ne ga kafirai!
20; Walkiyar tana yin kusa ta fizge gannansu, ko da yaushe ta haskaka musu, sai su yi tafiya a cikinta, kuma idan ta yi duhu a kansu, sai su yi tsaye. Kuma da Allah Ya so, sai Ya tafi da jinsu da gannansu. Lalle ne Allah a kan dukan kome Mai ikon yi ne.
21; Ya ku mutane! Ku bauta wa Ubangjinku, Wanda Ya halicce ku, ku da wadanda suke daga gabaninku, tsammaninku ku kare kanku !
22; Wanda Ya sanya muku kasa shimfida, kuma sama gini, kuma Ya saukar da ruwa daga sama, sa´an nan Ya fitar da abinci daga ´ya´yan itace game da shi, saboda ku. Saboda haka kada ku sanya wa Allah wasu kishiyoyi, alhali kuwa kuna sane.
23; Kuma idan kun kasance a cikin shakka daga abin da Muka sassaukar ga Bawanmu, to, ku zo da sura guda daga misalinsa (Alkur´ani). Kuma ku kirawo shaidunku baicin Allah, idan kun kasance masu gaskiya.
24; To, idan ba ku aikata (kawo sura) ba, to, ba za ku aikata ba, saboda haka, ku ji tsoron wuta, wadda makamashinta mutane da duwatsu ne, an yi tattalinta domin kafirai.
25; Kuma ka bayar da bishara ga wadanda suka yi imani. kuma suka aikata ayyuka na kwarai, chwa lallene, suna da gidajen Aljanna, koramu na gudana daga karkashinsu. Ko da yaushe aka azurta su da abinci daga wasu ´ya´yan itace daga gare su, sai su ce: "Wannan shi ne aka azurta mu da shi daga gabanin haka," Kuma a je musu da shi yana mai kama da juna, Kuma suna da, a cikin su, matan aure masu tsarki, kuma su, cikin su madawwama ne.
26; Lalle ne, Allah ba Ya jin kunyar Ya bayyana wani misali, kowane iri ne, sauro da abin da yake bisa gare shi. To, amma wadanda suka yi imani, sai su san cewa lalle shi ne gaskiya daga Ubangijin su, kuma amma wadanda suka kafirta, sai su ce: "Mhne ne Allah Ya yi nufi da wannan ya zama misali?" na batar da wasu masu yawa da shi, kuma Yana shiryar da wasu masu yawa da shi, kuma ba Ya batarwa da shi face fasikai.
27; Wadanda suke warware alkawarin Allah daga bayan kulla shi, kuma su yanke abin da Allah Ya yi umurni da shi a sadar, kuma suna barna a cikin kasa, wadannan su ne masu hasara.
28; Yaya kuke kafirta da Allah, alhali kuwa kun kasance matattu sa´an nan Ya rayar da ku, sa´nnan kuma Ya matar da ku, sa´an nan kuma Ya raya ku, sa´an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku?
29; Shi ne Wanda Ya halitta muku abin da ke a cikin kasa gaba daya, sa´an nan kuma Ya daidaita zuwa sama, sa´an nan Ya aikata su sammai bakwai. Kuma Shi ga dukan komai Masani ne.
1 COMMENTS
wapmash.xyzAbubakar Nuhu
June 22, 2020 AT 11:32 AM
Masha Allahu Nice Site

Leave a Reply

Name:


Comment: